Isa ga babban shafi

UNICEF ta yi tir da harin Sojin Habasha da ya kashe kananan yara a Tigray

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi tir da harin Sojin gwamnatin Habasha kan wata makarantar  yara da ya hallaka mutane 4 ciki har da kananan yara 2 a yankin Tigray na kasar.  

Wani sansanin 'yan gudun hijira a yankin Tigray na Habasha.
Wani sansanin 'yan gudun hijira a yankin Tigray na Habasha. AFP - EDUARDO SOTERAS
Talla

Tuni Gwamnatin Habasha ta musanta kaddamar da harin kan fararen hula, tana mai cewa dakarun Sojin saman ta sun yi luguden wuta ne a kan ‘yan tawayen TPLF ba wai a yankin da ke da kananan yara ba.

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi tir da farmakin wanda ta ce ya shafi tarin kananan yara da yanzu haka ke karbar kulawar gaggawa a asibiti.

Babbar daraktar UNICEF Catherine Russell cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce abin takaici yadda rikicin na Tigray ke ci gaba da shafar kananan yara.

Russell ta bayyana cewa sam bai kamata yakin bangarorin biyu ya rika shafar kananan yara ta kowacce fuska ba, musamman la’akari da yadda suka shafe kusan shekaru 2 suna cikin tsananin tashin hankali da bakar yunwa.

Harin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan dawowar yaki tsakanin ‘yan tawayen na Tigray da dakarun gwamnati da ke kawo karshen tsagaitawar watanni 5 da aka yi fatan ta kai ga kulla yarjejeniyar zaman lafiya.

Sanarwar da kungiyar ‘yan tawayen ta TPLF ta fitar ta ce harin Sojin saman na Habasha irinsa na farko cikin watanni 5 bayan makarantar kananan yaran da ya rushe ya kuma shafi gine-ginen fararen hular da basu ji ba basu gani ba.

Sai dai Habasha ta ce Sojinta sun kaddamar da farmakin ne kadai a sansanin ‘yan tawayen masu rike da makamai kuma babu fararen hula bare kananan yara a yankin.

Gwamnatin ta zargi ‘yan tawayen da nuna gawarwakin bogi don neman tausayawar duniya a rikicin da su da kansu ne suka janyo shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.