Isa ga babban shafi
Burundi

Ana shirin kirga kuri'un zaben shugabancin kasar Burundi

A Burundi a yanzu haka an kammala zaben shugabancin kasar, a yayin da aka soma kirga kuri’un bayan da al’umma suka wayi garin yau talata da karar bama bamai a Bujumbura babban birnin kasar, al’amarin da ya janyo asarar rayukan mutane biyu.

zaben shugaban kasa a Burundi
zaben shugaban kasa a Burundi PHOTO / PHIL MOORE
Talla

Al’ummar kasar ta Burundi dai sun fito sun jefa kuri’un su duk da cewa mazauna birnin Bujumbura sun tashi tare da jin karar bindiga da ma fashewar bama bamai al’amarin da ya kai ga rasa rayukan wasu mutane biyu.

Wannan ma dai ya biyo bayan kwashe tsawon watanni ana fama da rikice rikice sakamakon yunkurin shugaba Pierre Nkuruziza na sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku.

Ko da bayan yunkurin da wasu sojojin kasar suka yi na kifar da gwamnatin Nkurinziza a watan Mayu hakan bai hana shi janye takarar ba inda shugaban ya tsaya tsayin daka na ganin ya cimma burin sa.

An dai gudanar da zaben na yau duk da cewa yan adawa sun kaurace baki daya dama kiran da kasashen duniya yi ga gwamnati da ta dage zaben gudun hana kasar fadawa yakin basasa.

Mutane miliyan uku da dari takwas daga al’ummar kasar ce ke da damar jefa kuri’un su a zaben na yau,yanzu haka an soma kiddayar kuri'un.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.