Isa ga babban shafi
Burundi-AU

Wakilan gwamnatin Burundi sun ki halartar zaman tattaunawa da yan Adawa.

Ana sauran kwanaki biyu a gudanar da rikitacen zaben shugabancin kasar Burundi, tattaunawar da ake yi da nufin kawo karshen rikicin da kasar ta tsinci kanta a ciki tun karshen watan avrilun da ya gabata, tsakanin yan adawa da gwamnatin kasar an sake dage ta a yau lahadi, sakamakon rashin halartar wakilan gwamnatin kasar a zauren tattaunawar

tattaunawar kasar Burundi: ministan tsaron kasar Uganda, Crispus Kiyonga, tare da sakatare janar din kungiyar kasashen gabashin Afrika , Richard Sezibera.
tattaunawar kasar Burundi: ministan tsaron kasar Uganda, Crispus Kiyonga, tare da sakatare janar din kungiyar kasashen gabashin Afrika , Richard Sezibera. RFI/Sonia Rolley
Talla

Kasar Uganda dake shiga tsakani wajen ganin an warware rikicin ta hanyar tattaunawa, ta ce, bangaren shugaban kasar , cewa wakilan gwamnati da na jami’iyar dake mulkin kasar ta Burundi, basu halarci zaman tattaunawar ta yau lahadi ba, da ake gudanarwa a hotel Bujumbura al’amarin da ya tilasta daga zaman tattaunawar na yau

Masharhanta dai na ganin da gangan ne wakilan gwamnatin suka kauracewa tattaunawar ta yau, domin a ganinsu wata kila basu da abin cewa, a mahawarar  neman daga ranar gudanar da zaben shugabancin kasar da shugaba Nkronziza, dake son yin tazarce  a wani wa’adi na uku a jere  kan karagar shugabancin kasar ke son gudanarwa a ranar talata mai zuwa, duk kuwa da kiraye kirayen da kasashen duniya ke yi masa na kaucewa yin haka domin gudun jefa kasar cikin rikicin siyasa marar iyaka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.