Isa ga babban shafi
Burundi

Masu fada da juna a Burundi basu cimma matsaya ba

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya jagoranci tattaunawar sasanta rikici tsakanin bangarorin dake fada da juna a Burundi yayin da bangarorin biyu suka gaza cimma matsaya. 

Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni, da Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni, da Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza Photo: Sonia Rolley
Talla

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugancin Kasar Mako mai zuwa.

A cewar Museveni , Rikici a yankin Afrika da wasu sassa na duniya na faruwa ne sakamakon mummunar akida da muatne ke sanya wa kansu, yayin da mummunar akida ke kai ga aikata miyagun ayyuka, inda kuma miyagun ayyukan ke haifar da matsaloli.

Museveni ya kara da cewa, a farko Kasar Burundi ta kafu cikin tsari mai kyau tare da samun shugabanni na gari.

Museveni wanda tuni ya bar Bujumbura  ya ce, kokarin karbe iko daga hannun gwmanati  wata mummunar akida ce dake addabar al-ummar kasar, kuma ya gargadi cewa matukar 'yan siyasa suka ci gaba da haifar da rikice- rikice, to lallai Burundi ba za ta taba samun ci gaba ba.

Burundi dai ta tsinci kanta a halin rikici tun bayan sanarwar da Shugaban Kasar ya yi  Pierre Nkurunziza na sake tsayawa takara a wa’adi na uku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.