Isa ga babban shafi
Burundi

Jam’iyyar Nkurunziza ta lashe Zaben ‘Yan Majalisun Burundi

Hukumar Zaben kasar Burundi ta bayyana sakamakon zaben yan majalisar dokokin kasar da ke cike da rudani da aka gudana makwanni biyu da suka gabata, tare da bayyana jam’iyar shugaban kasar Pierre Nkurunziza a matsayin wacce ta lashe sama da kashi biyu bisa uku na yawan kujerun ‘yan majalisar dokoki.

'Yan adawa sun kauracewa zaben Burundi
'Yan adawa sun kauracewa zaben Burundi REUTERS/Paulo Nunes dos Santos
Talla

Jam’iyar CNDD-FDD da ke mulkin kasar Burundi ta samu nasarar lashe kujeru 77 daga cikin kujeru 100 da ake da su a majalisar dokokin kasar a sakamakon zaben ‘yan majalisun da ya gamu da suka na ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata, kamar yadda hukumar zaben kasar mai zaman kanta Ceni ta sanar a jiya Talata.

Hadin guiwar jam’iyun adawa da kuma ‘yan takara ma su zaman kansu karkashin jagorancin ‘yan adawa Agathon Rwasa da Charles Nditije, sun raba kujeru 20 ne a tsakaninsu.

A nasu bangaren Hadin guiwar ‘yan adawar dai sun bayyana kauracewa zaben ne sakamakon nuna rashin amincewa da tazarce da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ke shirin yi a wani sabon wa’adi na uku a jere kan karagar shugabancin kasar.

Sai dai kuma hukumar zaben ta ci gaba da sa su a zaben bisa abin da ta bayyana, babu wata bukata a rubuce daga 'yan adawar da ta bukaci cire sunayen ‘yan takarsu daga zaben na yan majalisar dokoki.

jam’iyun CNDD-FDD, l'Uprona da ke kawance da shugaba Nkurunziza sun lashe kujeru 2 ne kacal a majalisar dokokin kasar ta Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.