An kama makamai a kasar Burundi
Jami’an tsaro a kasar Burundi, sun kama mutane 100 bisa zargin su da cewa ‘yan tawaye ne;Yan Sanda sun sanar da karbe makamai da dama ga hanu wasu mutane, a wani mataki na dakile tashe tashen hankula a yayin da ake shirin gudanar da zaben shugabacin kasar.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawu hukumar Tsaron kasar Burundi ya bayana cewa Jami’an tsaron sun karbe kimanin bindigogi 30 a hannun mutanen da ake zargin yan tawayen ne a arewa maso gabashin lardin Muyinga.
Gwamanar lardin na Muyinga, Aline Maniratunga cewa ya yi an kama magoya bayan shugaban ‘yan adawa Agathon Rwasa a samamen da jami’an tsaron suka kai.
Rwasa , shi ne babban dan adawan Shugaban Kasar Pierre Nkrunziza, wanda ke neman zarce wa da mulki a wa’adi na uku.
A dai bangare , jami’an yan Sanda sun bayyana cewa sun kama sama da mutane 80 a areawci kasar Burundi sakamakon rikicin da ya barke a ranar juma’a da ta gabata kusa da iyaka da kasar Rwanda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu