Isa ga babban shafi
Burundi

Ana zaben shugaban kasa a Burundi

Al’ummar Burundi na gudanar da zaben shugaban kasa cikin fargaba inda ake sa ran shugaba mai ci Pierre Nkurunziza zai lashe zaben a wa’adin shugabanci na uku duk da kasashen duniya sun yi allawadai da matakin.

'Yan adawa sun kauracewa zaben Burundi
'Yan adawa sun kauracewa zaben Burundi PHOTO / PHIL MOORE
Talla

Rahotanni daga Bujumbura babban birnin Burundi na cewa wasu abubuwa sun fashe tare da jin karar harbin bindiga kafin bude runfunar zaben shugaban kasa.

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar akalla dan sanda guda a unguwar Musaga da ke birnin Bujumbura.

Kimanin mutane milyan uku da dubu dari takwas ke da ‘yancin kada kuri’a a zaben shugabancin kasar wanda mafi yawa daga cikin jam’iyyun adawa da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka yi kira da a kaurace.

Shugaban kasar mai ci Pierre Nkurunziza wanda ya sake tsayawa takara bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta ba shi damar yin haka, yana fuskantar suka daga abokan hamayyarsa na siyasa da kuma wasu kasashen duniya sakamakon sake tsayawa takara karo na uku.

Tun a watan Afrilu ‘Yan adawa ke gudanar da zanga-zangar adawa da matakin Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku wanda suka ce ya sabawa dokar kasa.

Mutanen Burundi sama da 150,000 suka tsere daga kasar zuwa makwabta don tsoron barkewar yakin basasa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.