Isa ga babban shafi
Yemen

'Yan tawayen Houthi sun yi watsi da kiran sakin jirgin ruwan Daular Larabawa

'Yan tawayen Houthi a Yemen sun yi watsi da bukatar Majalisar Dinkin Duniya da ta nemi su saki wani jirgin ruwa mai dauke da tutar kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da suka kwace a farkon wannan wata, bisa zargin yana dauke da makamai.

Jirgin ruwan Rawbee da mayakan Houthi suka kama a Yemen bisa. zargin yana dauke da makamai.
Jirgin ruwan Rawbee da mayakan Houthi suka kama a Yemen bisa. zargin yana dauke da makamai. - Oficina prensa hutíes/AFP
Talla

Wani jami'in Huthi Hussein al-Azzi ya ce " Jirgin ruwan na Rwabee ba ya dauke kayan wasan yara kamar yadda matuka jirgin suka bayyana, illa makamai da ake shirin jigilarsu da mayaka masu tsattsauran ra'ayi.

A ranar 3 ga watan Janairu, ‘yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan Iran suka kwace jirgin ruwan na Rawbee kusa da tashar ruwan birnin Hodeida, tare da ma’aikatanjirgin 11, sannan suka fitar da wani faifan bidiyo da suka ce ya nuna kayan ayyukan soja a cikinsa.

Yakin basasar kasar Yemen dai ya barke ne bayan da 'yan Houthi suka kwace babban birnin kasar Sana'a a shekara ta 2014, lamarin da ya sa sojojin da Saudiyya ke jagoranta suka shiga tsakani domin karfafa gwamnatin kasar a shekarar 2015.

Dubun dubatar mutane ne suka mutu, yayin da wasu miliyoyi suka rasa matsugunansu cikin yanayin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira tashin hankali mafi muni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.