Isa ga babban shafi
Yemen

Dakarun Saudiya sun halaka karin 'yan Houthi 138 a Yemen

Rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ta sanar da kashe 'yan tawayen Huthi 138 a cikin sa'o'i 24, a wani samame da ta jagoranci kaiwa a kusa da garin Ma'arib da ke hannun gwamnati.

Wasu mayaka masu biyayya ga rundunar hadin gwiwar da Saudiya ke jagoranta a yakin kasar Yemen. 27 ga Oktoba, 2021.
Wasu mayaka masu biyayya ga rundunar hadin gwiwar da Saudiya ke jagoranta a yakin kasar Yemen. 27 ga Oktoba, 2021. - AFP/File
Talla

A makwannin baya bayan nan dai kawancen sojin dake goyon bayan gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka amince da ita tun shekara ta 2015, sun rika bayar da rahoton kai hare-hare a kusan kullum kan mayakan na Houthi.

Sai dai ba kasafai ‘yan Houthin suke yin tsokaci kan fadan da suke gwabzawa da Saudiya kan birnin na Ma'arib ba, dake zama tungar gwamnati ta karshe da ta rage a arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, an lalata motocin soji 17, sannan an kashe 'yan tawaye 138 a yayin farmakin da jiragen yakin suka kai kan Al-Jubah dake kudancin Ma'arib da kuma Al-Kassara a arewa maso yammacin kasar ta Yemen.

Yakin basasar kasar Yemen dai ya barke ne bayan da 'yan Houthi suka kwace babban birnin kasar Sana'a a shekara ta 2014, lamarin da ya sa sojojin da Saudiyya ke jagoranta suka shiga tsakani domin karfafa gwamnatin kasar a shekarar 2015.

Dubun dubatar mutane ne suka mutu, yayin da wasu miliyoyi suka rasa matsugunansu cikin yanayin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira tashin hankali mafi muni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.