Isa ga babban shafi
Yemen

Harin bam ya kashe fararen hula 12 a Yemen

Fararen hula akalla 12 ne suka mutu yau Asabar a wani hari da ake kyautata zaton na bam ne da aka kai kusa da filin jirgin saman Aden, hedkwatar gwamnatin Yaman ta wucin gadi, kamar yadda wani babban jami'in tsaro ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Ma'aikatan agajin gaggawa na kasar Yemen a wurin da wani bam ya tashi kusa da filin jiragen saman birnin Aden, a ranar 30 ga Oktoba, 2021.
Ma'aikatan agajin gaggawa na kasar Yemen a wurin da wani bam ya tashi kusa da filin jiragen saman birnin Aden, a ranar 30 ga Oktoba, 2021. - AFP
Talla

Fashewar na zuwa ne kusan makwanni uku bayan kashe mutane shida a wani harin bam din da aka kai da wata mota kan tawagar gwamnan Aden wanda ya tsallake rijiya da baya.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin harin na ranar Asabar, wanda shi ne mafi muni tun watan Disambar bara, lokacin da aka kaiwa mambobin majalisar ministocin kasar harin bam a filin jiragen saman birnin na Aden.

A cikin 'yan makwannin da suka gabata dai, fada ya yi kamari a birnin Marib mai arzikin man fetur dake yankin arewacin kasar da ya rage a hannun gwamnati.

A baya bayan nan rundunar kawancen da Saudiya ke jagoranta ta sanar da kashe jimillar 'yan tawaye Houthi da Iran ke marawa baya kusan dubu 2,000 a kewayen birnin na Marib, a hare-haren da take kaiwa kusan kullum ta sama tun ranar 11 ga watan Oktoba.

Dubun dubatar mutane akasari fararen hula ne aka kashe tare da raba miliyoyi da muhallansu a yakin kasar Yemen, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta kira bala'in da ya tagayyara mutane mafi muni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.