Isa ga babban shafi
Yemen-Houthi

Dakarun kawance sun kashe 'yan tawayen Yemen 95 a kusa da Magrib

Dakarun kawancen da Saudiyya ke jagoranta da ke marawa gwamnatin Yemen baya, ta sanar da kashe 'yan tawayen Huthi 95 a wani hari ta sama da suka kai kusa da birnin Marib, mai matukar muhimmanci ga bangarorin biyu, a daidai lokacin da rikicin ke kara haifar da ‘yan gudun hijra.

Mayakan da ke goyon bayan gwamnatin Yemen sun nufi yankin da 'yan tawaye suke.
Mayakan da ke goyon bayan gwamnatin Yemen sun nufi yankin da 'yan tawaye suke. - AFP/File
Talla

Wannan sanarwa ta sanya adadin ‘yan tawayen Huthi  da kawancen ta kashe zuwa kusan dubu 2 a yankin na Magrib a hare-haren da take kai wa kussan kullum, tun daga ranar 11 ga watan Oktoba.

Sanarwar ta ce, rundunar hadin gwiwa ta kai hare-hare 22 kan 'yan tawaye a wasu yankuna biyu da ke kusa da Marib, inda suka kashe 'yan tawaye 95 tare da lalata motocinsu na yaki 11.

An kai harin bam na baya bayan nan a Al-Jawba mai tazarar kilomita 50 kudu da Marib da kuma Al-Kassara mai tazarar kilomita 30 daga arewa maso yammacin kasar.

Ba kasafai 'yan tawayen da Iran ke marawa baya ke yin tsokaci kan asarar da aka yi musu ba, kuma babu wata jarida mai zaman kanta da ta tabbatar da adadin.

Shi dai Marib, hedkwatar lardin mai arzikin man fetur dake arewacin Yemen, shi ne tungar karshe na gwamnatin kasar da kasashen duniya suka amince da shi.

Yakin kasar Yemen da aka fara tun a shekarar 2014, yayi sanadiyar hallaka dubban mutane yayin da wasu miliyoyi suka rasa matsugunansu a wani lamari da Majalisar Dinkin Duniya ta kira mafi muni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.