Isa ga babban shafi
RIKICI-YEMEN

Saudiya ta sanar da kashe wasu karin 'Yan tawayen Houthi 150 a Yemen

Dakarun Kawancen da Saudi Arabiya ke jagoranci sun sake sanar da hallaka ‘Yan Tawayen Houthi 150 a kusa da garin Marib dake kasar Yemen, sakamakon ci gaba da hare haren saman da suke kaiwa ba tare da kaukautawa ba, a yakin da aka kwashe shekaru 7 ana tafkawa.

Yan Tawayen Houthi a Yemen
Yan Tawayen Houthi a Yemen © AFP
Talla

Sanarwar da dakarun suka gabatar tace harin saman da suka kai ya lalata motocin soji 13 da ‘Yan tawayen suka mallaka tare da kashe mayakan su 150 a cikin sa’oi 24 da suka gabata.

Wannan sabon adadin ya nuna cewar ‘Yan tawayen da aka kashe a cikin yan kwanakin nan sun zarce 1,100 a kusa da Abdiya dake da nisan kilomita 100 daga Marib, cibiyar halartacciyar gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka amince da ita.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace ‘Yan tawayen Houthi basu cika mayar da martani akan irin asarar da suka tafka ba, kuma babu wata majiya ta daban da ta tabbatar da kisan.

A wata sanarwa da shugaban Yan Tawayen Abdelmalik al-Huthi ya gabatar ta kafar talabijin, ya bukaci magoya bayan sa da su ci gaba da fada domin abinda ya kira ‘yantar da Yankin su.

Dubban magoya bayan Houthi sun gudanar da zanga zanga yau a yankunan dake karkashin ikon su, inda suka sake jaddada goyan bayan su kare kasar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.