Isa ga babban shafi
Yemen-Houthi

Dakarun Larabawa sun kashe 'yan tawayen Houthi 156 a Yemen

Hadakar dakarun kasashen larabawa da ke yaki a Yemen karkashin jagorancin Saudiya ta sanar da kisan mayakan ‘yan tawayen Houthi fiye da 150 a yankin Marib na kasar.

Dakarun da ke yaki a yankin Marib na Yemen.
Dakarun da ke yaki a yankin Marib na Yemen. - AFP
Talla

Sanarwar hadakar da kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya wallafa ta ce yayin farmakin dakarun kan mayakan ‘yan tawayen masu samun goyon bayan Iran sun kuma lalata motocin yakinsu 8 baya ga jikkata mutane da dama.

A baya-bayan nan daruruwan mayakan na Houthi ne suka kwanta dama yayin fada kan birnin na Marib cibiyar yakin kasar ta Yemen kuma marika ta karshe dake hannun gwamnatin kasar daga arewaci.

Acewar hadakar cikin kasa da sa’o’i 24 dakarunta sun kai hare-hare ta sama kan ‘yan tawayen na Houthi har sau 33 a lardin Abdiya wanda ya hallaka mayakan 156.

Sanarawar hadakar karkashin jagorancin Saudiya, ta ce manufar hare-haren na da niyyar bayar da kariya ga fararen hilar da ke lardin na Abdiya.

Sai dai sanarwar ta bayyana yadda dakarun gwamnatin Yemen 17 suka rasa rayukansu a mabanbantan farmakin.

A watan jiya ne ‘yan tawayen na Houthi suka fara yunkurin kwace iko da Marib wanda yak ai ga rasa rayukan daruruwan dakaru galibi daga bangaren ‘yan tawayen masu samun goyon bayan Iran.

Shekarata 7 kenan Yemen na fama da yakin basasa wanda ya hallaka dubunnan daruruwan mutane ciki har da fararen hular da basuji ba basu gani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.