Isa ga babban shafi
RIKICIN-YEMEN

Saudiya ta sanar da kashe 'Yan tawaye 160 a Yemen

Kawancen sojojin da Saudi Arabia ke jagoranci wajen yaki da ‘Yan Tawayen Houthi dake kasar Yemen ya sanar da kashe ‘Yan Tawaye 160 a hare haren sama da ya kai Birnin Marib dake kudancin kasar.

'Yan Tawayen Houthi a fagen daga
'Yan Tawayen Houthi a fagen daga © AFP
Talla

Kamfanin dillancin labaran Saudiya ya jiyo majiyar sojin na cewar sun kai hare haren sama 32 a Abdiya a cikin sa’oi 24 da suka gabata, inda suka lalata motocin sojin ‘Yan Tawayen 11 da kuma hallaka ‘Yan Tawayen sama da 160.

Su dai ‘Yan Tawayen basu ce komai ba dangane da asarar da suka yi, kuma babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tabbatar da wannan adadi.

Birnin Marib dake Yemen
Birnin Marib dake Yemen - AFP/Archivos

Sanarwar kawancen sojojin ya bayyana cewar akalla ‘Yan Tawaye 700 suka kashe daga ranar Litinin zuwa yanzu sakamakon hare haren sama da suka kaddamar.

Garin Abdiya na da nisan kilomita 100 daga Marib, yayin da aka ruwaito cewar sauran ‘Yan Tawayen sun samu mafaka acan sakamakon munanan hare haren da aka kaddamar akan su.

Rahotanni sun ce an yi asarar akalla sojoji 20 da masu taimaka musu a fafatawar da suka yi a cikin sa’oi 24, yayin da wasu 47 suka samu raunuka.

Tsohon shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh da 'Yan Tawaye suka kashe
Tsohon shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh da 'Yan Tawaye suka kashe REUTERS/Yemen TV

‘Yan Tawayen Houthi sun kaddamar da hare hare wajen kwace iko a marib a watan Fabarairu, abinda yayi sanadiyar raba akalla mutane sama da 10,000 da muhallin su a watan Satumba kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.

Yakin basasa a Yemen ya barke ne a shekarar 2014 lokacin da ‘Yan Tawayen Houthi suka kwace iko da Birnin Sanaa, abinda ya sa Saudi Arabia ta kaddamar da yaki domin murkushe su.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukan su a yakin harda tsohon shugaban kasa Ali Abdallah Saleh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.