Saudiya ta sanar da kashe karin ‘yan tawayen Houthi 92 a Yemen
Dakarun kawancen da Saudi Arabia ke jagoranta sun sanar da kashe karin ‘yan tawayen Houthi 92 a wani sabon harin ta sama da suka kaddamar kan yankuna biyu dake birnin Marib a kasar Yemen.
Wallafawa ranar:
‘Yan tawayen Houthin na baya bayan nan da suka halaka a baya bayan nan, na daga cikin cikin daruruwan da dakarun kawancen n a Saudiya suka sanar da kashewa a hare haren da suka kaddamar ta sama a birnin na Marib da kewaye.
Kamfanin dillancin labaran Saudiya ya ce bayan mutane 92 da aka kashe, dakarun sun kuma lalata motocin soji 16 a Yankin Al Jawba da Al Kassara.
A ranar Litinin 18 ga watan Oktoban da muke, kawancen sojojin da Saudiya ke jagoranci wajen yaki da ‘yan tawayen Houthi ya sanar da kashe mayakan Houthin 160 a hare haren sama da ya kai kan birnin Marib dake kudancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu