Isa ga babban shafi
UNICEF-Yemen

Cikin shekaru 6 an kashe kananan yara dubu 10 a Yemen- UNICEF

Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce rikicin kasar Yemen ya hallaka ko kuma jikkata kananan yara akalla dubu 10 cikin shekaru 7 da aka shafe ana gwabza yakin.

Wasu tarin kananan yara da rikici ya tagayyara a kasar Yemen.
Wasu tarin kananan yara da rikici ya tagayyara a kasar Yemen. - AFP
Talla

UNICEF a wani taron manema labarai da ta gudanar a Geneva ta ce rikicin na Yemen ya sake kaiwa wani mataki mafi kunyatarwa a duniya bayan gano yadda ya shafi kananan yara dubu 10 lamarin da kakakin asusun James Elder ke cewa akwai bukatar kawo karshen yakin don ceto miliyoyin kananan yara da ke halin tagayyara.

UNICEF ya ce tun bayan faro yakin a watan Maris din shekarar 2015 kananan yara dubu 10 ne yanzu haka ko dai suka mutu ko kuma suka samu muggan raunuka sanadiyyar rikicin, alkaluman da ke nuna rasa ran yara 4 a kowacce rana cikin kasar ta Yemen a tsawon sehkarun 6.

Kakakin na UNICEF y ace alkaluman iya wanda suka iya tattarawa ne yayinda ake da tarin wadanda rikicin ya shafa ba tare da sun iya samun alkaluman ko bayan ikan faruwar lamarin ba.

Acewarsa UNICEF na bukatar fiye da dala miliyan 235 don ci gaba da ayyukan jinkai a sassan kasar ta Yemen zuwa nan da tsakiyar shekarar 2022.

Elder ya ce matukar asusun ya gaza samun wannan adadin kudi, ko shakka babu ayyukansa za su iya dakatawa a Yemen said ai ya ce ko da anyi nasarar samun kudaden dole akwai bukatar kawo karshen yakin don ceto rayukan da ke ci gaba da salwanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.