Isa ga babban shafi
Yemen-Houthi

Saudiya ta sake kashe mayakan Houthi 105

Saudiyya ta yi ikirarin hallaka mayakan Houthi har guda 105, a wani barin wuta da ta yi musu ta sama a sansanoninsu da ke kasar Yemen.

Wasu mayakan 'yan tawayen Houthi a birnin Sanaa na kasar Yemen.
Wasu mayakan 'yan tawayen Houthi a birnin Sanaa na kasar Yemen. AP - Hani Mohammed
Talla

Saudiyya dai ta sha bada sanarwar kashe mayakan na Houthi, duk da yadda mayakan ke ikirarin kwace kusan dukannin manyan garuruwa a Yemen.

Da wannan kisan dai a yanzu Saudiyya ta halaka mayakan Houthi kusan dubu 2 a hare-hare ta sama da ta ke bada sanarwar kai wa kusan kullum tun ranar 11 ga watan Octoban da muke ciki.

Kungiyar ta Houthi da ke samun goyon bayan Iran ba kasafai take bada sanarwar mutuwar mambobinta ko kuma wani hari da aka kai wa mambobin ta ba.

Sai dai a wannan karon ‘yan Houthin sun ce suna ci gaba da fadada ayyukan tsaron su, a ciki da kewayen babban birnin kasar Magrib.

A harin da Saudiyyan ta yi ikirarin kaiwa din, ta kuma lalata motocin sojoji da 'yan tawayen suka kwata guda 13 a hare-haren da aka kai yankin Al-Jawba mai nisan kilomita 30 da birnin Magrib da kuma Al-Kassara dake da nisan Kilomita 30 da iyakar kasar ta yankin arewa maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.