Farmakin 'yan tawayen Huthi kan masallaci ya hallaka mutane 22 a Marib
Akalla mutane 22 sun mutu a farmakin 'yan tawayen Huthi na Yemen da suka harba makami mai linzami kan wani masallaci da ke kudancin birnin Marib a kasar.
Wallafawa ranar:
Alkaluman dakarun Sojin da ke samun goyon bayan gwamnatin kasar ya nuna yadda farmakin ya hallaka fararen hula 22 tare da jikka wasu 19 ciki har da kananan yara.
Bayanai sun ce cikin daren jiya ne mayakan na huthi suka farmaki masallacin wanda ke yankin Al-Jawba matsayin martini kan hare-haren da sojoji masu samun goyon bayan kassahen larabawa ke kai musu.
Dubunnan mayakan na Huthi suka rasa rayukansu a ‘yan kwanakin nan sakamakon yadda dakarun larabawa karkashin jagorancin Saudiyya ke ci gaba da tsananta hare-hare kansu.
Wasu alkaluma da ma’aikatar yada labarai ta Yemen ta wallafa a shafinta na Twitter ta ruwaito ministan labarai Moammar al-Eryani na cewa mutane 29 suka rasa rayukansu a farmakin kan masallaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu