Isa ga babban shafi
Yemen

Mayakan Houthi sun kashe dakarun Sudan 14 a Yemen

Wata majiyar sojan Yemen ta ce sojojin Sudan akalla 14 sun rasa rayukansu, a wani hari da 'yan tawayen Houthi suka kai a kusa da kan iyakarsu da Saudiyya daga bangaren arewa maso yamma.

Wasu sojojin kasar Sudan da ke taimakawa Saudiya a yakin kasar Yemen.
Wasu sojojin kasar Sudan da ke taimakawa Saudiya a yakin kasar Yemen. © Getty Images
Talla

Majiyar sojin ta Yemen ta ce an kashe sojojin na Sudan ne lokacin da mayakan suka kai farmaki kan wasu yankunan Haradh da ke lardin Hajja a ranar Alhamis.

Sudan dai na cikin rundunar kawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka amince da ita tun shekara ta 2015, inda take gwabza yaki da yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran.

Tun da jimawa ne dai kasar Sudan ta aike da dubban sojoji zuwa Yemen, ciki har da mayakan Janjaweed da suka yi kaurin suna kan zargin da ake musu na aikata munanan laifuka a yakin basasar da ya barke a yankinta na Darfur a shekara ta 2003.

Sai dai a karshen shekarar 2019, gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta ce za ta rage yawan dakarunta a Yemen daga 15,000 zuwa 5,000.

Rikicin Yemen da ya faro tun a shekarar 2014 bayan 'yan tawayen Huthi sun kwace babban birnin kasar Sanaa, ya haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira tagayyarar jin kai mafi muni a duniya.

Miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu kuma fiye da kashi 80 na al'ummar kasar ta Yemen kusan miliyan 30 na bukatar agajin jin kai, yayin da mutane akalla dubu 377 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.