Isa ga babban shafi
Yemen

An kashe mayakan Huthi dubu 15 a Yemen

Kusan mayakan Huthi da ke kasar Yemen dubu 15 ne aka kashe a kusa da birnin Marib tun daga watan Yuni, kamar yadda majiyoyin da ke kusa da ‘yan tawayen suka tabbatar, yayin da aka dauki tsawon shekaru bakwai ana rikici a kasar.

Wasu daga cikin mayakan Huthi a Yemen
Wasu daga cikin mayakan Huthi a Yemen AFP
Talla

Wani jami'in ma'aikatar tsaro da ke karkashin ikon 'yan tawayen ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, hare-haren ta sama da kawancen sojan da Saudiya ke jagoranta suka kaddamar ya yi sanadin mutuwar 'yan Huthi dubu 14,700 tun a tsakiyar watan Yuni.

A bangaren gwamnatin kasar kuma ta ce, sama da dakarunta  dubu 1 da 200 ne aka kashe a cikin watanni biyar yayin da suke kare yankunan da ke kusa da Marib, kamar yadda wasu jami’an sojan gwamnati biyu suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa.

Birnin Marib dai shi ne birni na karshe da gwamnatin kasar ta amince da shi a arewacin kasar Yemen mai arzikin man fetur.

An sha zaman tattaunawa domin kawo karshen rikicin, amma 'yan tawayen sun sake sabunta hare-harensu a watan Fabrairu, inda a watan Yuni ma suka kai wani mummunan hari, al’amarin da ya kara tsananta tun watan Satumba.

Wani kawance da kasar Saudiyya ke jagoranta na shiga tsakani a shekara ta 2015 don tallafa wa gwamnati, tun daga ranar 11 ga watan Oktoba, ya bayar da rahoton cewa kusan kowace rana ana kai hare-hare ta sama a kusa da Marib tare da adadin wadanda suka mutu, bisa ga kididdigarsu, kusan 'yan tawaye 3,800.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.