Isa ga babban shafi

Canada ta taimakawa falesdinawa da kudi domin sake gina Gaza

Kasar Canada tace zata aike da kayan agaji na Dala miliyan 25 domin taimakawa Falasdinawan dake Gaza da Gabar Yamma da Kogin Jordan mako guda bayan kawo karshen tashin hankalin da aka yi tsakanin su da Isra'ila wanda yayi sanadiyar rasa dimbin rayuka.

Yankin Gaza dake karkashin Falesdinu
Yankin Gaza dake karkashin Falesdinu AP - John Minchillo
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Marc Garneau yace za’a mika agajin ga Majalisar Dinkin Duniwa wanda ya kunshi Dala miliyan 10 domin samar da abinci da ruwan sha da kuma gyara gidajen da suka rushe, yayin da kuma za’ayi amfani da Dala miliyan 10 wajen samar da magunguna da kuma kayan more rayuwa.

Gine-ginen da hare-haren Isra'ila ya ruguza a yankin Gaza na Falasdinawa 27 ga watan Mayun 2021
Gine-ginen da hare-haren Isra'ila ya ruguza a yankin Gaza na Falasdinawa 27 ga watan Mayun 2021 AP - John Minchillo

Sanarwar gwamnatin tace za’ayi amfani da Dala miliyan 5 wajen aikin gina zaman lafiya da zummar ganin an samu kwanciyar hankali a Yankin Gabas ta Tsakiya baki daya.

Akalla Falasdinawa 254 suka mutu a rikicin da aka kwashe kwanaki 11 anayi, yayin da Israila tayi asarar soja guda da fararen hula guda 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.