Isa ga babban shafi
Falestinu-Israel

Falesdinawa na shirin kiran babban taron majalisar kolinsu

A yau ne ake sa ran Babbar hukumar cin gashin kan falestinawa zata yanke shawarar kiran babban taron majalisar kolin falastinu (CNP), wace rabonta da ta gudanar da taro yau shekaru 20 ke nan da suka gabata kamar yadda wani jami’in palastinawan ya sanar

Shugaban kungiyar Hamas ta Falestinawa , Khaled Mechaal,
Shugaban kungiyar Hamas ta Falestinawa , Khaled Mechaal, AFP PHOTO / KHALIL
Talla

zaman taron da ake ganin zai haifar da sauye sauye ga daukacin hukumar cin gashin kan na falestinawa

A dai gefen kuma a jiya ne, shugaban kungiyar Hamas mai mulkin ziri Gaza Khaled Mechaal, ya fito fili ya bayyana cewa, kungiyar na tattaunawa da kasar Israela wajen samar da yarjejeniyar tsagaita buda wuta ta tsawon lokaci

Wannan ikrari nasa dai ya tabbatar da zargin da hukumar cin gashin kan Falestinawa ta PLO ta yi ne, cewa Hamas na kokarin raba yankunan na palastinawa gida 2 ta hanyar mikawa izraela wuya
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.