Isa ga babban shafi
Isra'ila-Gaza

Sojojin Isra'ila sun kashe wasu Falesdinawa a Jordan

Sojojin Isra’ila sun kashe wasu Falasdinawa guda hudu bayan sun yi kokarin abka masu a yamma da kogin Jordan.A makon da ya gabata rikici ya barke tsakanin Falasdinawa da Sojojin Isra’ila a birnin Hebron da ke yankin yamma da Kogin Jordan, a yayin da Falasdinawan suka yi jana’izar ‘yan uwansu matasa biyar da suka rasa rayyukansu a arangama da Jami’an tsaron na Isra’ila.  

Wani shigen jami'an tsaro a zirin Gaza
Wani shigen jami'an tsaro a zirin Gaza REUTERS/Mussa Qawasma
Talla

Wanann dai na zuwa ne bayan jami’an Isra’ila da ke kula da kan iyaka sun bindige wani Bafalasdine har lahira a wajen binciken ababan hawa, inda suka ce ya yi yunkurin daba wa daya daga cikinsu wuka.

Tun bayan da tarzomar ta fara a watan jiya a birnin Kudus, kawo yanzu Falasdinawa 66 sun rasa rayyukansu, inda Yahudawa suka rasa mutane tara.

Rundunar sojin Isra’ila tace Falesdinawan sun yi kokarin dabawa jami’an Sojin wuka, lamarin da ya sa aka harbe su.

Faladdinawa uku ne Sojojin na Isra’ila suka kashe a wata mahada a yankin Gush Etzion kudu da birnin Kudus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.