Isa ga babban shafi
Palestine

Tarzoma ta barke tsakanin Palasdinawa da Jami'an Isra'ila

Rikici ya barke tsakanin Palasdinawa da Sojojin Isra’ila a birnin Hebron da ke yankin yamma da Kogin Jordan, a yayin da Palasdinawan suka yi jana’izar ‘yan uwansu matasa biyar da suka rasa rayukansu a arangama da Jami’an tsaron na Isra’ila.

Palasdinawa 66 ne suka rasu, inda yahudawa suka rasa mutane 9 tun bayan faruwar rikicin a watan jiya.
Palasdinawa 66 ne suka rasu, inda yahudawa suka rasa mutane 9 tun bayan faruwar rikicin a watan jiya. REUTERS/Mussa Qawasma
Talla

Wanann dai na zuwa ne bayan jami’an Isra’ila da ke kula da kan iyaka sun bindige wani Bafalasdine har lahira a wajen binciken ababan hawa, inda suka ce ya yi yunkurin daba wa daya daga cikinsu wuka.

Tun bayan da tarzomar ta fara a watan jiya a birnin Kudus, kawo yanzu Palasdinawa 66 sun rasa rayukansu, inda Yahudawa suka rasa mutane tara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.