Isa ga babban shafi

Kotu ta soke nasarar wanda zai tsaya wa PDP takara a zaben gwamnan Zamfara

A Najeriya, Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Zamfara ta sanar da soke zaben fidda gwani, wanda a lokacinsa aka sanar da Alhaji Dauda Lawal Dare a matsayin wanda zai tsaya wa PDP takarar gwamna a zaben da a yi cikin shekara mai zuwa.

Zamfara na cikin tashin hankalin hare-haren 'yan bindiga
Zamfara na cikin tashin hankalin hare-haren 'yan bindiga © Channels
Talla

Wani tsohon dan majalisar tarraya ne Alhaji Ibrahim Shehu Gusau ne ya shigar da kara a gaban kotun, inda ya bukaci a soke zaben saboda a cewarsa an tafka kura-kurai.

A lokacin da yake yanke hukunci a wannan Juma’a, mai shari’a Aminu Baffa Aliyu, ya bayyana amincewa da illahirin korafe-korafen da mai shigar da kara ya gabatar.

A martaninsa jim kadan bayan sanar da wannan hukunci, lauyan mai shigar da kara Barrister Ibrahim Ali, ya ce hukuncin ya dace, lura da irin hujjojin da suka gabatar wa kotu.

Da aka nemi jin matsayinsa dangane da wannan hukunci, mai bai wa jam’iyyar PDP shawara a game da lamurran da suka shafi shari’a Barrister Bashir Abubakar Masama, ya ce za su yi nazarin wannan hukunci kafin yanke shawara a game da matakin da suke ganin cewa ya dace a gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.