Isa ga babban shafi

PDP kada kuri'ar amincewa da Ayu a matsayin shugaban kwamitin amintattu

Kwamitin zartaswa na jam'iyyar PDP na kasa ya amince da kuri'ar amincewa da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na kasa ya kasance karkashin jagorancin Dakta Iyorchia Ayu.

Dakta Iyorchia Ayu
Dakta Iyorchia Ayu © punch
Talla

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Ndudi Elumelu ne ya gabatar da kudirin amincewa wanda ya samu goyon bayan Ishola Balogun Fulani daga jihar Kwara.

Shugaban kwamitin amintattu, Sanata Adolphus Wabara, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya sanya ayar tambaya kan wanda ya ki amincewa da kudirin, amma mafi rinjayen mambobin sun amince da a kada kuri’ar amincewa da Ayu.

Ndudi ya ce sun dauki wannan mataki ne saboda irin yadda suka jagoranci jam’iyyar wajen lashe zaben gwamnan jihar Osun da kuma jagorantar jam’iyyar ta hanyar da ta dace.

A halin da ake ciki, yayin da yake gabatar da jawabinsa, Ayu ya ce, "Ina so in fara wannan taro ta hanyar sanar da cewa shugaban kwamitin amintattu, ya yanke shawarar yin murabus. Ya yi wa wannan jam’iyya hidima da gaskiya har ya kai matsayin Sakataren kwamitin da kuma shugaba na kasa.”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.