Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta yi amai ta lashe game da harajin tsaro na yanar gizo 'internet'

Babban bankin Najeriya CBN ya dakatar da batun umarnin cire harajin tsaro na yanar gizo da ya baiwa bankunan kasar da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade.

Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja.
Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

 

Babban Bankin Najeriya ya janye umarnin da ya bayar na neman bankuna da sauran cibiyoyi da ke gudanar da hada-hadar kudade da su rika cire harajin tsaro na yanar gizo kamar yadda aka tsara a cikin Dokar samar da  Kariya da Hana Laifukan Intanet na 2024.

Babban bankin ya sanar da hakan ne a wata takarda da aka yi wa kwaskwarima ranar 17 ga Mayu, 2024 wacce ta bukaci yin hakan.

Sanarwar wacce Daraktan kula da shige da ficen kudi na babban bankin, Chibuzor Efobi tare da Daraktan Sashen Tsare-tsaren Kudi, Haruna Mustafa, suka sanya wa hannu, an gabatar da ita ne ga bankunan kasuwanci, da masu hada-hadar kudade biyan (PSPs) da sauran su.

Umarnin tattara harajin ya co karo da kalubale a fadin kasar wanda ya sa fadar shugaban kasar ta dakatar da aiwatar da tsarin.

Majalisar zartaswar Najeriya ta dakatar da aiwatar da wannan dokarce saboda bukatar da ke akwai wajen ci gaba da nazarinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.