Isa ga babban shafi

Gamnatin Najeriya na shirin kara kudin karatu a manyan makarantu

Gwamnatin Najeriya na shirin bullo da biyan kudaden karatu a manyan makarantun kasar, biyo bayan rattaba hannu kan kudirin bayar da rance ga dalibai da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanyawa hannu.

Wasu dalibai da ke kokarin ficewa daga jami'ar Legas kenan, bayan umarnin da aka basu.
Wasu dalibai da ke kokarin ficewa daga jami'ar Legas kenan, bayan umarnin da aka basu. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A ranar litinin ne aka rattaba hannu kan kudirin dokar, yayin da ‘yan kasar da dama suka nuna farin ciki da hakan, ba tare da fahimtar ma’anar sabuwar dokar ba ga miliyoyin daliban da ke neman gurbin karatu da suka dogara da shirin karatu kyauta a manyan makarantun kasar.

Masana ilimi da sauran masu ruwa da tsaki sun ce hakan zai haifar da kalubale ga karatun dalibai.

A Najeriya, kudin makaranta da y afara daga naira dubu dari ko ma miliyoyin nairori a jami'o'i masu zaman kansu, kyauta ne a makarantun gwamnati kama daga matakin tarayya ko kuma jihohi.

Lamarin dai ya kasance tun bayan samun ‘yancin kai, duk da cewa ana biyan kudade a wasu lokutan kamar wurin kwanan dalibai, sashe, da rajistar kwas, da sauransu .

Bayar da tallafin karatu dai ya baiwa miliyoyin dalibai damar zuwa makaranta, sai dai masu lura da al’amura na ganin bullo da shirin bayar da lamuni na dalibai da gwamnatin tarayya ta yi na nufin kawo karshen karatun dalibai kyauta.

A cewar dokar ba da lamuni ga dalibai, hakan zai samar da sauki ga ‘yan Najeriya masu karamin karfi ta hanyar samun lamuni marar kudin ruwa daga asusun bayar da lamuni na ilimi na Najeriya, domin inganta karatun matasan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.