Isa ga babban shafi

Duk da mutuwar malamanmu 10 ba zamu bada kai bori ya hau ba - ASUU

Shugaban kungiyar malaman jami’oin Najeriya reshen Jami’ar Calabar, Dr John Edor, yace ba zasu taba bada kai bori ya hau ba, wajen janye yajin aikin da suke yi, duk da rasuwar 10 daga cikin malaman su da suka rasu a makarantar.

Tambarin ASUU a Najeriya
Tambarin ASUU a Najeriya The Herald Nigeria
Talla

Wata sanarwar da shugaban ya rabawa manema labarai tace, babu gaskiyar cewar malaman jami’ar 21 ne suka mutu saboda radadin yajin aikin da suke yi.

Dakta Edor, yace tabbas sun rasa 10 daga cikin su da suka hada da farfesoshi guda 5, cikin su harda Farfesa Gabriel U. Ntamu da Farfesa Judith Otu da Farfesa Udosen da Farfesa Kate Agbor da kuma Farfesa Obia tare da wasu malaman da basu kai mukamin Farfesa ba guda 5.

Shugaban kungiyar malaman yace zasu ci gaba da jajircewa wajen yajin aikin har zuwa lokacin da zasu cimma muradunsu na tilasta gwamnatin tarayya biya musu bukatunsu na inganta jami’oin kasar.

Dakta Edor yace suna sane da yunwa da barazana da kuma umurnin kotun da aka basu, amma ba zasu taba bada kai bori ya hau ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.