Isa ga babban shafi
Najeriya - Kimiyya

An samu bullar sabuwar manhaja mai barazana ga Komfutoci da wayoyin hannu - NCC

Masana kimiya da fasaha sun yi gargadin cewa wata sabuwar manhaja mai hatsarin gaske dake illa ga Komfuta da sauran na’urori masu alaka da ita da ake kira da Flubot na yawo a yanzu haka.

Na'urar Komfuta
Na'urar Komfuta © Reuters
Talla

Manhajar da ake kira da Virus ko Malware a turance ana tsara ta ne musamman don lalatawa, ko kuma yi wa na’urar Komfuta kutse ta kowane hali.

A wannan Juma’ar ce dai Hukumar Sadarwar Najeriya NCC ta fitar da sanarwar dake fadakar da miliyoyin masu amfani da na’urorin Komfuta da kuma wayoyin hannu dangane da barazanar muguwar manhajar ta Flubot a Najeriya.

Hukumar ta NCC ta ce ta samu bayanai kan barazanar ce daga kwamitin kar ta kwana dangane da lamurran na’ura mai kwakwalwa na Najeriya kan cewa manhajar ta Flubot na kai hari kan wayoyin hannu na Android da sauran dangoginsu ta hanyar fakewa da kokarin baiwa bayanan mutane kariya ko kuma tallata musu sabbin manhajoji.

A cewar daraktan hulda da jama'a na NCC, Dakta Ikechukwu Adinde, Flubot ana kwaikwayon aikace -aikacen manhajojin hada-hadar banki da wayoyin hannu na Android ke amfani da su, sai dai burinsa shi ne satar bayanan mutane da kuma sace kudaden dake asusunsu na bankuna idan ya samu dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.