Na'urar James Webb ta kammala tafiyar makwanni 2 zuwa tashar sararin samaniya
Na'urar hangen nesa ta James Webb da aka harba zuwa sararin samaniya cikin kumbon ‘yan sama jannati, ta kammala tafiyar makwanni 2 a jiya Asabar, inda ta isa tashar da za ta fara aikin nazarin kimiyya kan tarihin sararin na samaniya.
Wallafawa ranar:
Bayan daidaituwar na’urar binciken da James Webb dai, kwararru da suka kula da aikin harba ta a cikin kumbon 'yan sama Jannati sun yi ta sowa a Cibiyar Kimiyya ta binciken halittun sama wadda ke Baltimore, a Maryland dake kasar Amurka.
Masana kimiya na ganin cewa, na’urar ta James Webb za ta taimaka wajen tattaro karin bayanai game da asalin halittu da sauran duniyoyi.
Na’urar ta James Webb wadda aka kashe mata biliyoyin kudi na Dala wajen kera ta, ta doron kasar da muke ne daga cibiyar aikin kimiya ta Kourou da ke yankin Guiana na Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu