An gano hotunan abin da ya faru shekaru biliyan 13 a sararin samaniya
Katafariyar na’urar hangen nesa ta James Webb, ta dauko wasu hotunan sararin samaniya, wadanda ba a taba ganin irinsu ba da suke fayyace wasu daga cikin al’amuran da suka wakana shekaru biliyan 13 da suka gabata kan halittun sararin samaniya.
Wallafawa ranar:
Daya daya daga cikin hotunan da na’urar ta aiko a Talatar nan, ya nuna alamun ruwa a cikin kunshin iskar da ke zagaye da wata sabuwar duniya mai cike da iskar gas wadda aka gano a shekarar 2014.
Sabuwar duniyar mai suna WASP-96 mai nisan tafiyar haske na tsawon shekaru dubu 1 da 400 daga duniyar da muke, tana da kwatan-kwacin rabin nauyin duniyar Jupiter, kazalika tana zagaya babbar tauraruwar da take a matsayin rana ta cikin kasa da kwanaki hudu, kwatan-kwatanci shekara guda a duniyarmu.
Wani karin hoton da fadar White House ta fitar wanda na’urar ta James Webb ta dauko, ya kuma nuna dubun-dubatar curin duniyoyi da ke rarrabe a yankunansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu