Isa ga babban shafi

Bafaranshiyar marubuciya Annie Ernaux ta lashe lambar yabo ta Nobel

Marubuciyar kasar Faransa Annie Ernaux, ta samu lambar yabo ta Nobel, inda ta kasance mace ta biyu a cikin mutane takwas da suka samu lambar yabon a bana.

Bafaranshiya marabuciya Annie Ernaux
Bafaranshiya marabuciya Annie Ernaux © AFP
Talla

Tana daya daga cikin fitattun marubuta da suka shiga takarar neman lambar yabo.

Annie mai shekaru 82 ta kasance Bafaranshiya ta 17 da ta samu wannan lambar yabo, haka zalika a cikin mata ita ce ta goma sha shida a duniya da suka samu kyautar.

Littatafanta sun yi fice ne saboda iya tsara magana wajen rubuce-rubucen ta, kuma littafinta na farko an buga shi ne a shekarar 1970 mai suna Emty cupboard, wanda ke fadakarwa kan illar da zubar da ciki ba bisa ka’ida ba ke haifarwa.

A cikin rubuce-rubucen ta akwai wanda ake ganin abin kunya ne a rubuta, kamar littafinta na baya-bayan nan mai suna The Young Man, wanda ke bayyana wata soyayya mai cike da sarkakiya kan wani matashi da ke soyayya da wata tsohuwa da ta girme shi da shekaru talatin.

Annie ta gaji marubucin kasar Tanzania Abdulrazak Gurnah, wanda ya lashe kyautar a 2021, bisa rubuce-rubucen da ya yi kan mulkin mallaka da kuma kaura ba bisa ka’ida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.