Isa ga babban shafi

Jami'ar kimiya da Fasaha ta Dangote dake Wudil a jihar Kanon Najeriya ta sarrafa sakandami AI

Jami’ar kimiya da fasaha ta Aliko ta jihar Kano da ke Wudil da ake kira da jami’ar kimiyya da fasaha ta Dangote na kirkirar sakandami da su rika gudanar da ayyukan share-share da goge da kuma sauran ayyuka na yau da kullum a cikin makarantar.

sakandami, na'urar da ake sanaywa basirar dan'adam
sakandami, na'urar da ake sanaywa basirar dan'adam QUENTIN TYBERGHIEN / AFPTV / AFP
Talla

 

Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Musa Yakasai ya bayyanawa manema labaru cewa wannan sakandami da ake dorawa basirar dan’adam zai taimakawa ma’aikata a yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Ya ce hukumar gudanarwar jami’ar ta samu kyakkyawar nasara matuka  akan fasahar kere-kere da amfani da fasahar sadarwa don baiwa dalibai damar yin amfani da ita gaba daya da kuma kasancewa a cikin wannan sabon tsari da ke tashe a duniya.

Farfesan ya kara da cewa an jaraba sakandamin kuma ya yi abin da ake da bukata kamar yadda aka tsara shi.

Ya kuma ci gaba da cewa Jami’ar zata ci gaba da irin wadannan kirkire-kirkiren na na’urori domin zasu taimaka wajen sauwake aikace-aikace dake daukar lokaci da kuma  wahalarwa a tsakanin ma’aikata..

Mataimakin shugaban Jami’ar ya ce makarantar ta yi gyaran wasu dakunan karatu na zamani da zai baiwa dalibai damar samun cikakkiyar fasaha ta sarrafa sakandaman da sauran na’urori da zasu taka rawa wajen gogayya da sauran cibiyoyi na duniya a fannin samar da na’urorin da ake hasashen zasu taka rawa a muhallan al’uma.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.