Isa ga babban shafi
Twitter

Twitter na bincike kan kutsen da aka yi wa fitattun mutane

Kamfanin Twitter na gudanar da bincike kan gagarumin kutsen da wasu ‘yan damfara suka yi wa rumbunan bayanai na fitattun mutane da suka hada da tsohon shugaban Amurka Barrack Obama da fitaccen attajirin nan, Bill Gate da kuma wasu manyan kamfanoni irinsu Apple da Uber.

Wasu 'yan damfara sun yi wa shafukan fitattun mutane kutse a Twitter domin damfarar jama'a
Wasu 'yan damfara sun yi wa shafukan fitattun mutane kutse a Twitter domin damfarar jama'a REUTERS/Kacper Pempel/Illustration/File Photo
Talla

Daga cikin wadanda kutsen ya shafa har da Joe Biden, dan takarar Jam’iyyar Demokrat a zaben shugabancin Amurka mai zuwa da Elon Musk da kuma Kanye West.

Sai dai wannan kutsen bai shafi rumbun bayanan shugaban Amurka Donald Trump ba wanda ke da kimanin mabiya miliyan 83 a shafinsa na Twitter.

Kamfanin Twitter ya bayyana cewa, ‘yan damfarar sun yi amfani da asusun wasu ma’aikatan Twitter domin samun damar kutsawa cikin rumbunan fitattun mutanen da kamfanoni.

Wata kafar yada labarai da ake kira VICE ta rawaito cewa, wani ma’aikacin Twitter ne aka hada baki da shi wajen yin kutsen, tana mai dogaro da wasu hotunan Screenshot da kuma boyayyun majiyoyi da suka shaida mata cewa, masu damfarar sun biya ma’aikacin na Twitter kudi.

A sakwannin zambar da suka wallafa, masu damfarar sun bukaci jama’a da su aiko da Dala dubu 1 na kudin Bitcoin cikin minti 30, sannan a mayar musu da ninkin kudin daga bisani.

Mutane sun tura jumullar Bitcoin 12.58, kwatankwacin Dala dubu 116 zuwa ga adireshin da ‘yan damfarar suka yi amfani da shi kamar yadda shafin Blockchain mai kula hada-hadar kudin intanet ya sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.