Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka ta zargi Rasha da yi mata kutsen na'ura tare da sace muhimman bayanai

Gwamnatin Amurka ta tabbatar da rahoton cewa an yi mata kutse a hanyoyin sadarwar na'urorita, bayan da jaridar ‘The Washinton Post’ ta ruwaito cewa akalla ma’aikatun kasar 2 masu kutse daga Rasha suka kai wa farmaki.

Jami'an tsaron FBI na ci gaba da bincike kan wasu kungiyoyi da ake zargin suna da hannu a farmakin.
Jami'an tsaron FBI na ci gaba da bincike kan wasu kungiyoyi da ake zargin suna da hannu a farmakin. Scott Olson/Getty Images/AFP
Talla

Jaridar ‘The Washington Post’ ta ce kutsen da aka yi na da nasaba da wadanda aka yi a makon da ya gabata a kan wani kamfanin da ke sa ido a kan masu kutsen intanet na FireEye, wanda ya ce wasu shu’uman masu kutse sun hargitsa musu matakan tsaro, inda suka sace wasu manhajoji da su ke amfani da su wajen gwajin komfutocin abokan huldarsu.

Kamfanin na FireEye ya ce yana zargin wata kasa ce ta dau nauyin wannan kutse.

Kakakin hukumar tsaron kafar intanet na Amurka, ya ce suna aiki sau da kafa da abokan huldar hukumomin kasar a game da kusten da aka gano wasu sun yi wa hanyoyin sadarwar gwamnati.

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa hukumar tsaron FBI na binciken wasu kungiyoyi da ke aiki da hukumar leken asirin kasa da kasa ta Rasha, suna mai cewa an shafe tsawon watanni ana wannan kutse.

Sai dai ofishin jakadancin Rasha a Amurka ya mayar da martani cikin fushi, inda ya nesanta kansa da al’amarin kutsen, yana mai cewa labarin kanzon kurege ne daga kafafen yada labaran Amurka, kuma manufofinta da fahimtar ta na huldar kasa da kasa sun yi hannun riga da hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.