Isa ga babban shafi
Nobel-Tanzania

Dan Afrika ya lashe kyautar Nobel bangaren marubuta

Haifaffen Tanzania, Abdulrazak Gurnah ya lashe kyautar Nobel bangaren marubuta sakamakon rubutun da ya yi game da rayuwa bayan mulkin mallakar turawa da kuma halin da ‘yan cirani ke tsintar kansu a ciki, nasarar da ta bashi damar zama dan Afrika na 5 da ya taba lashe kyautar ta Nobel bangaren marubuta.

Abdulrazak Gurnah wanda ya lashe kyautar marubuta ta Nobel.
Abdulrazak Gurnah wanda ya lashe kyautar marubuta ta Nobel. via REUTERS - CHAPTER OF CANTERBURY CATHEDRAL
Talla

Abdulrazak Gurnah haifaffen Tanzania da ya tashi a yankin Zanzibar gabanin komawa Ingila cikin ‘yan cirani a 1968, an haifeshi ranar 20 ga watan Disamban 1948 ya kuma faro karatunsa a cikin kasar gabanin juyin juya halin yankin na Zanzibar da ya kai ga kwace ikon yankin daga hannun larbawa wanda kuma ya haddasa kwararar tarin ‘yan cirani zuwa sassan Duniya.

Gurnah ya ci gaba da karatu a kwalejin Chris Church da ke karkashin jami’ar London inda ya samu digirin farko.

Gurnah ya kammala PhD a shekarar 1983 inda ya yi koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya tsakanin shekarun 1980 zuwa 1982.

Har zuwa lokacin ritayarsa, Farfesa Gurnah ya ci gaba da aiki da jami’ar Kent inda ya yi aiki tare da fitattun marubuta na Duniya ciki har da V.S Naipaul da Salman Rushdie da kuma Zoe Wicomb yayinda ya taka muhimmiyar rawa a mujallar Wasafiri tun daga 1987.

Gurnah na daga cikin jerin farfesoshin Afrika da suka kware a rubutun Zube inda ya yi rubuce rubuce masu muhimmanci da suka kunshi Paradise a 1994 da kuma Desertion a 2005 kana By the Sea a 2001 littattafan da dukkaninsu ya samu lambar yabo a kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.