Isa ga babban shafi
Nobel

An fara bayar da kyautar Nobel ga kwararru a duniya

An fara baiwa wasu fitattaun mutane da suka taka rawa a fannoni da dama lambar yabo ta Nobel, inda wasu kwararru a fannin da ya shafi lafiya da suka hada da David Julius da Aderm 'yan asalin kasar Amurka suka lashe kyautar.

Mutanen da suka kasance a sahun gaba wajen fara karbar kyautar a bana.
Mutanen da suka kasance a sahun gaba wajen fara karbar kyautar a bana. Cléa PÉCULIER AFP
Talla

Bisa al’ada dai, akan zabi wasu fitattaun mutane a duniya da suka taka rawa a fannoni da dama don ba su wannan lambar yabo ta Nobel mai matukar muhimmanci.

A bana, an fara bayar da kyautar ce daga fannin kimiyya da lafiya, inda za a ci gaba da bayar da ita a  na fannin har-hada magunguna a gobe Talata, sai fannin har-hada sinadarai da za a bada a  ranar Laraba.

Za a bayar da kyautar a  sashen adabin Turanci wato Literature a ranar Alhamis, sai na zaman lafiya wadda kusan ita ta fi kowacce muhimmanci da za a bayar da ita a ranar Litinin na makon gobe.

Kamar kowanne fanni dai, cutar Corona ta shafi tsarin bayar da kyautar yabon da ake yi kowacce shekara, sai dai duk da an yi a bana, amma dai an kula sossai wajen tara jama’a da kuma tabbatar da biyayya ga dokokin kare yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.