Wasu kwararru sun lashe Nobel saboda binciken sauyin yanayi
Masanin Kimiyyar Nauyin Kwayar Zarra dan asalin Japan, amma mazaunin Amurka, Syukuro Manabe da takwarorinsa na Jamus da Italiya, wato Klaus Hasselmann da kuma Giorgio Parisi sun lashe kyautar Nobel saboda bajintar da suka nuna a fannin ilimin kimiya tare da gano hanyoyin da za’a magance matsalolin sauyin yanayi.
Wallafawa ranar:
Kwamitin bada kyautar ta Nobel, ya ce, wannan kyautar da aka mika wa masana kimiyar, tamkar zaburar da sauran kasashen duniya ne, a daidai lokacin da ya rage ‘yan makawanni ,a gudanar da babban taron sauyin yanayi, a birnin Glasgow.
Manabe, mai shekaru 90 da Hasselmann mai shekaru 89, za su raba Dalar Amurka miliyan daya da dubu 100 a tsakaninsu, yayin da na ukunsu wato Parisi mai shekaru 73 ya samu rabin kyautarsu.
Kyautar ta biyo bayan binciken da suka gudanar ne a kan sauyin yanayi kuma suka yi zarra ga sauran takwarorinsu a wannan bangare.
A cewar kwamitin, masu binciken sun kafa tubalin da al’umma za ta jima tana mora a kan yanayi da kuma yadda mutane ke bada gudunmawa wajen sauya shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu