Isa ga babban shafi
China-Faransa

China ta yi tayin tura dakaru 500 zuwa Mali

Kasar China ta yi tayin tura Karin sojojinta sama da 500, don bayar da tallafi ga dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke yakar ‘yan tawayen kasar ta Mali. Wannan ne mafi yawan sojan da China ke tura wa a wani aikin kawo zaman lafiya a duniya.

Dakarun kasar China
Dakarun kasar China 2.bp.blogspot.com
Talla

Jami’an jakadanci, da ma kwararru na kallon wannan matakin, a matsayin neman kawo karshen kallon hadarin kajin da ke tsakanin kasar ta China da wasu kashen yammacin duniya, sakamakon takun sakan da ake yi kan rikicin kasar Syria.

Matakin zai kuma taimaka wajen karfafa dangantaka tsakanin kasar ta Sin da kashen nahiyar Africa, inda take a gaba-gaba wajen sayen danyen man fetur da sauran ma’adinai.

Kasar Fransa, da ta fara jagorantar yakin na Mali a watan Janairu, na fatan mika ragamar jagorantar dakarun wanzar da zaman lafiyan da ke aiki a kasar, a watan Yuli.

Yanzu haka fiye da sojojin Nahiyar Africa 6,500 ne ke aiki a kasar ta Mali, kuma Majalisar Dinkin Duniya na bukatar karin akalla dakaru 3,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.