China/Sin
India da China sun yi alkawarin kulla abota mai karfi
Primiyan kasar Sin Li Keqiang, da ke ziyara a India, ya ya yi alkawarin kulla abota mai karfi tsakanin kasashen biyu.
Wallafawa ranar:
Talla
Bayan tattaunawar da suka yi da mai masaukin nashi Manmohan Singh a yau litinin, Li ya ce dangantaka tsakanin kasashen biyu da ke da karfin tattalin arziki a Nahiyar Asiya, za ta taimaka wajen samar da zaman lafiya a duniya.
Ya ce dalilin da ya sa ya zabi India a matsayin kasar da ya fara ziyarta shine muhimmancin da hukumomin Birnin Beijing ke kallon dangantaka da Delhi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu