Isa ga babban shafi

Bakin alkalami ya bushe kan janye tallafin man fetur - Tinubu

Sabon Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewar gwamnatinsa ba zata biya kudin tallafin da ake sanyawa a man fetur ba, abinda ya tabbatar da kawo karshen shirin tallafin baki daya, kamar yadda ya shaidawa jama’a lokacin yakin neman zaben sa. 

Bola Ahmed Tinubu, lokacin da yake karbar rantsuwar aiki.
Bola Ahmed Tinubu, lokacin da yake karbar rantsuwar aiki. © RFI/bashir
Talla

Tinubu yace zai yi amfani da wadannan kudade da ake zubawa tallafin wajen gudanar da wasu manyan ayyukan raya kasa, yayin da ya jinjinawa gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gabace shi saboda daukar matsayin kawo karshen biyan tallafin da yace masu hannu da shuni ne kawai ke amfana da shi. 

Yayin da yake jawabi bayan karbar rantsuwar fara aiki, shugaban yace zasu karkata irin wadannan kudaden da ake biyan tallafin da su wajen gina kayan more rayuwa da bunkasa ilimi da harkokin kula da lafiya da kuma kirkiro ayyukan yin da zai taimaki miliyoyin jama’a. 

Sabon shugaban wanda yace zai sake duba fasalin sauya kudaden da Babban Bankin kasar ya aiwatar wanda ya jefa jama’ar kasar cikin halin kunci, yace zai kuma duba matsalar da ake samu wajen dorawa kamfanoni haraji har sau biyu, domin bada damar bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma janyo hankalin masu zuba jari. 

Tinubu ya sha alwashin samar da hukumar da zata dinga kayyade farashin kayayyaki da kuma bunkasa harkar noma da kiwo ta yadda zai dada bunkasa tattalin arzikin Najeriya. 

Yace ta wannan hanyar ce za’a sama da abinci wadatacce kuma mai sauki, yayin da manoma zasu ci gajiyar ayyukan da suke yi, jama’a kuma su samu abinci a farashi mai rahusa. 

Sabon shugaban ya bayyana aniyarsa ta hada kan ‘yan Najeriya, inda yake cewa da wadanda suka zabe shi da wadanda basu zabe shi ba, daga yankin Neja Delta, zuwa sararin sahara da birnin Lagos zuwa Abuja da Onitsha duk mutanensa ne. 

Tinubu yace a matsayinsa na shugaban kasa, zai gudanar da aiki ba tare da nuna banbanci ga wani bangare ba, yayin da yace zasu zuba kudade wajen inganta tsaro wanda shine abu na farko da zai mayar da hankali akai domin cimma biyan bukata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.