Isa ga babban shafi

Wakilan jam'iyyu sun fice daga cibiyar tattara sakamakon zaben Najeriya

Wakilan manyan jam’iyyun adawa a cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa da ke Abuja sun fice daga wurin taron domin nuna adawa da yadda ake sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.

Yadda ake tattara sakamakon zaben shugabancin Najeriya a Abuja kenan.
Yadda ake tattara sakamakon zaben shugabancin Najeriya a Abuja kenan. © RFI
Talla

Dino Melaye da Emeka Ihedioha na PDP sun zargi INEC da karya dokar zabe ta hanyar ci gaba da tattara sakamakon zabe da sanarwa duk da rashin shigar da sakamakon a na’urar iREV.

Wakilan wasu jam’iyyu da suka hada da na SDP da LP da ADP sun bayyana irin wannan ra’ayi.

Wakilan da suka fusata duk sun fita daga wurin taron.

Shugaban INEC Mahmood Yakubu ya yi watsi da bukatar wakilan inda ya ce za a ci gaba da sanar da sakamakon zaben jihohin kasar da aka kada a ranar Asabar da Lahadi.

Daga nan ne INEC ta ci gaba da aikin tattara sakamakon zaben kasar.

“Ba mu zo nan don mu kalli magudin zaben da INEC da APC suka bayyana ba,” in ji Dino Melaye ga manema labarai.

“Ana yiwa INEC zagon kasa. APC ta yi tasiri sosai akan INEC,” inji shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.