Isa ga babban shafi

Obama ya roki 'yan siyasar Najeriya da su tabbatar an yi sahihin zabe

Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, ya roki ‘yan takaran zaben shugaban kasar Najeriya tare da shugabannin jam’iyyun siyasa da su ba da gudumawa wajen ganin an gudanar da karbaben zabe cikin kwanciyar hankali a karshen wannan mako. 

Tsohon shugaban kasar Amurka Barrack Obama.
Tsohon shugaban kasar Amurka Barrack Obama. REUTERS/Jason Reed
Talla

A sakon da ya aikewa jama’ar kasar dake shirin zuwa zabe, Obama yace Najeriya ta fada cikin tsaka mai wuya amma kuma ta samu nasara a matsayin ta na kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka. 

Tsohon shugaban ya bayyana wannan zabe a matsayin wata damar rubuta wani sabon tarihi na ci gaban kasar ta fuskar siyasa, yayin da ya bukaci jama’ar Najeriya da su jinjinawa kansu akan wannan nasarar da aka samu. 

Obama yace ‘yan Najeriya sun bada gudumawa wajen samun ‘yancin kai da kuma sanya kasar akan tafarkin dimokiradiya bayan kwashe dogon lokaci ana mulkin soji, tare da kuma inganta rayuwar iyalai da gina tattalin arzikin kasa. 

Tsohon shugaban yace yanzu ga wata dama ta samu na rubuta wani sabon babi dangane da zabe mai zuwa, kuma ana samun nasarar zabe ne idan an gudanar da shi ba tare da tinzira jama’a tashin hankali ko kuma yin wani abinda zai kawar da sahihancinsa ba. 

Obama yayi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su gudanar da zabukansu cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata matsala ba 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.