Iran ta sake musanta zargin cewa tataimakawa Rasha da makamai
Iran ta nisanta kan ta daga cikin kasashen da ke baiwa Rasha makamai da za ta yi amfani da su a yakin Ukraine, kasar da sojojin Rasha suka mamaye.
Wallafawa ranar:
kyiv da kawayenta na Yamma suna zargin Moscow da yin amfani da jirage marasa matuka da Iran ta kera wajen kai hare-hare kan Ukraine a makonnin da suka gabata. A litinin ake sa ran za a tattauna batun a taron ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar turai a Luxembourg.
Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ya musanta zargin da ake masa, ya kuma ce kasarsa ba ta bayar da makaman da za a yi amfani da su a yakin Ukraine ba, a cewar wata sanarwa da ma'aikatarsa ta fitar.
A ranar Litinin da ta gabata, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce an kai hare-hare da dama da ya ce ta hanyar amfani da makamai masu linzami na Iran da jirage marasa matuka, tare da aukawa makamashin Ukraine.
A wata ganawa ta daban da shugaban diflomasiyyar Turai Josep Borrell, Mr. Amir-Abdollahian ya jaddada matsayin Iran a hukumance kan yakin Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu