Isa ga babban shafi

Dubban mutane ne suka yi zanga-zangar adawa da mulkin soji a Sudan

Dubban masu zanga-zanga a Sudan sun fito kan tituna a ranar Talata, domin neman a koma mulkin farar hula bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a bara inda suka yi kira ga sojoji da su koma barikinsu.

Masu zanga-zangar dai na kiran sojoji su koma bariki
Masu zanga-zangar dai na kiran sojoji su koma bariki AP - Marwan Ali
Talla

Sudan dai na fama da zanga-zanga tun bayan da dakarun da ke karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan suka kwace mulki a watan Oktoba.

Kwace mulkin ya kara sauye sauye ga mulkin farar hula wanda aka kaddamar tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekara ta 2019, bayan shafe shekaru talatin yana mulkin kasar.

Har ila yau, sun dauki hotunan wasu mutane 116 da likitoci suka ce an kashe a wani farmakin da aka kai kan masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin.

Matsalar tattalin arziki ta kara tsananta a Sudan wadda ke fama da talauci bayan juyin mulkin da ya haifar da raguwar taimakon agaji na kasa da kasa.

Ma’aikatan gwamnati, ‘yan kasuwa, leburori da ma’aikatan jinya da dai sauransu sun kara yin suka kan tsadar rayuwa da karancin albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.