Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Dambarwar siyasa a Nigeria
Bayanan da ke fitowa na cewa tuni aka fara buga kugen siyasa Nigeria, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kasar ko korafi kan matsalolin rayuwa, da rashin tsaro da sauran su.Sai dai Gwamnatin kasar na cewa ta yi rawar gani a cikin shekara da rabi, na wa'adin wannan gwamnati.wannan shine abin da za mu duba a shirin DUNIYAR MU A YAU, na wannan makon, wanda Bashir Ibrahim Idris zai gabatar, a yi saurare lafiya.05/01/201320:30 -
Tsokacin 'Yan Siyasa ga ci gaban da aka samu a 2012 a Najeriya
‘Yan Siyasa a Najeriya na ci gaba da tsokaci kan zaben shekarar 2015, yayin da hotunan shugaba Goodluck Jonathan suka mamaye wasu sassan biranen kasar. A cikin Shirin Duniyarmu a Yau za ku ji Muharawa tsakanin Ministan yada labarai, Labaran Maku, da Buba Galadadima na CPC game da ci gaban da aka samu a 2012.05/01/201320:30 -
Matsalar koma bayan yankin Arewacin Nijeriya
Yanzu haka ana ta kokarin samar wa arewacin Nijeriya sabuwar makoma. Wannan na zuwa ne sakamakon yadda yankin ke komawa na baya ga dangi.Ababen da yankin ke tinakaho da su a baya, da suka hada da dawwamammen zaman lafiya, tsaro, albarkar gona, ingantaccen ilimi, adalci da girmama na gaba, sun zama tarihi.Maimakon wadancan, yanzu ba abin da ke addabar sassa daban-daban na yankin sune tashe-tashen hankula, kashe-kashen kabilanci da na addini, matsalar ilimi, talauci da watsi da aikin gona da suka mamaye yankin.Shirin DUNIYAR MU A YAU, na wannan makon, ya duba wannan batun, kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masu ruwa da tsaki daga yanki na arewacin Nijeriya.Shirin ya kuma leka fagen siyasar kasar ta Nijeriya, inda ya duba muhimman batutuwa a yankin na arewa.... a yi saurare lafiaya.22/12/201222:18 -
Dambarwar Siyasar Ghana da rikicin Mali da Masar
Shirin Duniyarmu A Yau ya yi bayani ne tare da 'Yan Jarida kamar kullum game da dambarwar siyasar kasar Ghana da kuma Rikicin kasar Mali da zanga-zangar adawa da matakin sabunta kundin tsarin mulkin kasar Masar.15/12/201220:13 -
Zaben Shugaban kasar Ghana
Shirin Duniyarmu A Yau ya yi bayani ne game da Zaben Shugaban kasar Ghana da aka gudanar a ranar 7 ga watan Disemba.08/12/201220:56 -
Nasarar Falasdinawa a Zauren MDD
A ranar 29 ga watan Nuwamba ne Falasdinawa suka samu nasarar samun kujerar 'Yan kallo a zauren Majalisar Dinkin duniya bayan kwashe shekaru suna gwagwarmaya duk da adawar Isra'ila da Amurka. Shirin Duniyarmu A yau ya tattauna ne game da wannan batu.03/12/201221:34 -
Rikicin Isra'ila da Falesdinawa a Gaza
Shirin Duniyarmu A yau ya yi tsokaci ne game da rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas a zirin Gaza inda tun daga ranar 14 ga watan Nuwamba bangarorin biyu suka ta kai wa juna hare hare. Bashir Ibrahim Idris da abokan shirin shi sun tattauna game da rikicin.25/11/201220:54 -
Obasanjo yace Najeriya na fuskantar Barazanar Juyin juya hali
Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo yace Najeriya na fuskantar Barazanar juyin juya hali a wata Ziyara da ya kai a Birnin Dakar na kasar Senegal a taron samar wa matasa aikin yi. Shugaban yace Matasan Najeriya na fuskantar matsalar rashin aikin yi. A Cikin Shirin Duniyarmu A yau Bashir Ibrahim Idris da abokan shirin sun yi tsokaci game da kalaman na Obasanjo.17/11/201220:51 -
Obama ya yi tazarce a Amurka
Shugaban Amurka Barack Obama ya lashe zaben Shugaban kasa wa’adi na biyu bayan samun kuri’u mafi rinjaye a jahohin Ohio da Wisconsin wanda ya ba shi damar doke Mitt Romney na jam’iyyar Republican. Tuni dai Mitt Romney ya taya Obama Murna ta wayar Salula tare da amsa shan kaye. Bashir Ibrahim Idris tare da abokan shirin Duniyarmu A yau sun tattauna game da nasarar da Obama ya samu10/11/201222:36 -
Zaben Shugaban kasar Amurka
A ranar Talata mai Shida ga Watan Nuwamba Al'ummar kasar Amurka za su kada kuri'ar zaben Shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci, Barack Obama, na Jam’iyar Democrat, da Mitt Romney na Jam’iyar Republican. Game da Zaben ne Shirin Duniyarmu A Yau ya tattauna akai saboda matukar tasirin Zaben ga 'Yan kasar Amurka, da ma al’ummar duniya baki daya.03/11/201222:12 -
Yajin aikin Direbobi a Nijar
Shirin Duniyarmu A Yau ya yi bayani ne game da yajin aikin Direbobin Motocin Sufuri saboda rashin amincewa da rage kudaden Man Fetir da Gwamnatin Nijar ta yi wanda ya saba wa bukatunsu. Wannan ne kuma ya sanya al'ummar Nijar cikin wani mawuyacin hali. Bashir Ibrahim Idiris Tare da abokan shirin sun tattauna game da wannan batu.21/10/201220:27 -
Rikicin Najeriya da Bakassi
Shirin Duniyarmu A yau ya tattauna ne game da rikicin Bakassi tsakanin Najeriya da Kamaru.13/10/201220:10 -
Nazarin ci gaban Najeriya a shekaru 52
A ranar daya ga watan Octoba ne, Najeriya za ta yi bukin cika shekaru 52 da samun ‘Yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma Wasu na cewa har yanzu tana da sauran tafiya, idan aka kwatanta kasar da sauran kasashen da suka samu ‘Yancin kai tare. A cikin Shirin Duniyarmu A Yau, Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari game da matsalolin Najeriya tare wasu tsoffin shugabanin kasar.08/09/201221:00 -
Gurbacewar Al'adar Bahaushe
Shirin Duniyarmu A Yau ya tattauna ne da Farfesa Bunza na Jami'ar Danfodio a Sokoton Najeriya game da gurbacewar Al'adar Bahaushe a kasar Hausa.25/08/201220:00 -
'Yancin yankin Ogoni a Najeriya
A ranar biyu ga watan Agusta ne kungiyar da ke ikrarin fafutukar ‘Yantar da Yankin Ogoni, mai arzikin man fetur, suka sanar da yancin cin gashin kai, kamar yadda shugaban kungiyar ta MOSOP, Goodluck Diigbo, ya sanar, inda ya ke cewa daga yanzu sun zama yanki mai ‘Yanci a Najeriya. Wasu mutanen Yankin da dama sun yaba da wannan mataki, wanda suke ganinsa a matsayin wani abinda zai basu damar mallakar arzikin man da ke Yankin, da kuma gina al’ummar su. Bashir Ibrahim Idris tare da abokan shirin Duniyarmu A yau sun tattauna game da wannan batu.12/08/201222:03
Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.