Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Duniyarmu A yau: Harin Baga da ke cikin jihar Borno
A shirin Duniyarmu A Yau na wannan mako, Bashir Ibrahim Idris tare da bakinsa, sun tattaunawa ne a game da harin da aka kai garin Baga na jihar Borno a Tarayyar Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 180.27/04/201320:06 -
Kwamitin tattaunawa da Boko Haram
Shirin Duniyarmu A Yau ya tattauna ne a game da kwamitin da shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa domin bayar da shawarwari kan yadda za a kwance wa kungiyar Boko Haram damara.20/04/201320:18 -
Yunkurin yi wa Boko Haram afuwa
Bayan Matsin lamba daga shugabanni da Sarakuna, da malaman addini da kuma wasu masu fada aji a Najeriya, shugaban kasa Goodluck Jonathan ya “bada kai bori ya hau”, wajen sauya ra’ayinsa kan matakin matakin yi wa Kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Lida’awati wal Jihad, da ake kira Boko Haram, Afuwa inda ya kafa kwamitin da zai bashi shawara akai. Shirin Duniyarmu A Yau ya duba wannan dambarwa da kuma fatar da ake da shi.07/04/201320:09 -
Juiyin mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
A shirin Duniyarmu a Yau na wannan mako, Bashir Ibrahim Idris da kuma wasu 'yan jarida, sun tattauna ne a game da juyin mulkin da ya faru a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.30/03/201320:03 -
Ziyarar Obama a Gabas ta Tsakiya
Karo na farko Barack Obama ya kai ziyara a Isra'ila da yankin Falasdinu, a game da haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wasu 'yan jarida.23/03/201320:48 -
Zaben Kenya
Shirin Duniyarmu a yau ya tattauna ne da 'yan jaridu a game da zaben Kenya wanda Bashir Ibrahim Idris ya jagoranta.16/03/201320:58 -
Mutuwar shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez
Shirin Duniyarmu a yau ya tattauna ne kan batun mutuwar shugaba Hugo Chavez, wanda rasuwarsa kamar yadda masana ke bayyanawa ta haifar da babban gibi ga shugabancin kasar ta Venezuela.09/03/201321:14 -
Tattaunawa da El Rufa'i game da Littafinsa
Tsohon Ministan Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya, Malam Nasiru El- Rufa'i ya wallafa wani Littafi mai suna “Accidental Public Servant'” a Turance, wanda ya gabatar a birnin Lagos bayan fara kaddamar da litaffin a Abuja inda a cikin littafinsa ya yi bayani akan aikinsa da huldarsa da Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo. A Hirar shi da Bashin Ibrahim Idris ya bayyana dalilin rubuta littafin da kuma alakar litaffin da dambarwar siyasar Najeriya.02/03/201320:05 -
21:02
-
Murabus din Fafaroma Benedict na Goma Sha Shida daga mukaminsa
Tattaunawa kan Murabus din Fafaroma Benedict na Goma Sha Shida daga mukaminsa.16/02/201322:05 -
Gasar Cin kofin Afrika
'Yan wasan Super Eagles na Najeriya suka lashe kofin Afrika karo na uku bayan doke 'Yan wasan Stallions na Burkina Faso ci 1-0 a wasan karshe da aka gudanar a kasar Afrika ta Kudu. Shirin Duniyarmu A Yau ya tattauna ne game da gasar cin Kofin Afrika da aka gudanar karo na 29.09/02/201321:12 -
Tattaunawa akan hukunci da kotu ta yankewa John Yusuf Yakubu akan kudaden fansho
Tattaunawa akan hukuncin da kotu ta yankewa Darektan Hukumar kula da kudin fansho na 'Yan sandan Najeriya, John Yusuf Yakubu.02/02/201320:01 -
An rantsar da Obama Wa'adi na biyu a Amurka
Shirin Duniyarmu A yau ya tattauna ne da 'Yan Jaridu game da batun rantsar da Shugaban Amurka Barack Obama a wa'adi na Biyu.26/01/201321:30 -
Faransa da ECOWAS sun kaddamar da yaki a Mali
A Cikin Shirin Duniyarmu A Yau, Bashir Ibrahim Idris tare da Abokan shirin shi sun tattauna game da Yakin da Faransa da Kasashen Yammacin Afrika suka kaddamar a Mali20/01/201320:21 -
Dambarwar Siyasar Venezuela
Shirin Duniyarmu A Yau na mako ya yi bayani game da dambarwar siyasar kasar Venezuela tsakanin magoya bayan Hugo Chavez da ke kwance a gadon Asibiti da kuma 'Yan adawa.13/01/201320:32
Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.