Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Dambarwar siyasar Jihar Taraba bayan dawowar Gwamna Dan Baba Suntai
A watan Oktoban bara ne Gwamnan Jihar Taraba, Dan Baba Suntai ya samu hadarin jirgi, lamarin da ya sa ya fita kasar waje domin neman magani, wanda hakan ya sa aka ba mataimakinshi Alhaji Garba Umar damar tafiyar da ragamar mulkin Jihar. A kuma farkon makon da ya gabata ne, Gwamna Suntai ya dawo daga jinya, lamarin da har ila yau ya haifar da kace - nace a daukacin Najeriya yayin da Suntai ya yi yunkurin ci gaba da aiki. To sai dai Majalisar Dokokin Jihar, wacce ta ziyarci gwamnan ta dakile wannan yunkuri na shi ta na mai cewa bai samu cikakkiyar lafiyar da za a mayar mai da ragamar tafiyar da mulkin jihar ba. Akan wannan batu shirin Duniyramu A Yau ya tattauna.31/08/201321:21 -
Matsalar ambaliyar ruwa a arewacin Najeriya
Ambaliyar ruwa na ci gaba da yin ta'adi a sassa daban-daban na arewacin Najeriya.Wannan na zuwa ne duk kuwa da kashedin hukumar kula da yanayi ta NIMET ta yi, game da wannan batu tun a farkon shakara. Wannan shine abin da Bashir Ibrahim Idris dab akin shi, suka duba mana a cikin shirin na Duniyar Mu A Yau, na wannan mako, sai a biyo su, don jin shirin.A yi saurare lafiya.24/08/201320:14 -
Hira da Janar Buhari: Yadda jama'iyyar APC ke kokarin fafatawa a zabukan Najeriya
A watan da ya gabata hukumar zabe ta Najeriya INEC, ta yiwa Jama'iyyar adawa ta APC rajista, inda jama'iyyar ta ce yanzu ta kimtsa, don fafatawa a zabukar kasar masu zuwa.bayan samun wannan rajista, me ya rage wa wannan sabuwar jama'iyyar? Wannan ita ce tambayar da Bashir Ibrahim Idris ya nemi jin amsar ta, a cikin shirin Duniyar a Yau, kuma ya sami ganawa da tsohon shugaban Najeriyar, kuma tsohon dan takarar shugabancin kasar, a zaben shekarar 2011.Sai a biyo mu cikin wannan shirin, don jin yadda tattaunawar tasu ta kaya, a yi saurare lafiya.17/08/201320:35 -
Rikicin siyasar kasar Masar
Dubban magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi na ci gaba da gudanar da zanga-zanga duk da gargadin da gwamnatin rikon kwarya ta yi zata dauki matakin watse sansaninsu.Wanan shine abin da shirin Duniyar mu a yau na wannan makon zai duba, inda Abdulkarim Ibrahim da bakin nashi suka yi nazari kan wannan badakalar, ayi saurare lafiya.10/08/201320:12 -
Mugabe ya lashe zaben Zimbabwe
Hukumar zabe a Zimbabwe ta bayyana sunan Shugaba Robert Mugabe a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, yayin da babban mai adawa da shi Morgan Tsvangirai, ya sha alwashin kalubalantar sakamakon zaben, wanda Amurka tace an yi magudi. Garba Aliyu tare da abokan shirin Duniyarmu A Yau sun tattauna game da zaben.03/08/201319:31 -
Zaben Shugaban kasa a Mali
Shirin Duniyarmu A Yau ya yi bayani ne game da zaben shugaban kasa da aka gudanar karo na farko a kasar Mali bayan sojoji sun kifar da gwamnatin farar hula ta Amadou Toumani Toure, Shugabannin kasashen duniya da suka hada da shugaban Faransa sun yaba da yadda aka gudanar ba tare da samun wani tashin hankali ba. Bashir Ibrahim Idiris ya tattauna wannan batu tare da abokan shirin shi.27/07/201320:28 -
Kotun Duniya ta cika shekaru 15
A ranar 17 ga watan Yuli ne Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta cika shekaru 15 da kafuwa wacce aka kafa domin hukunta laifukan yaki na bai daya a duniya. Wannan kuma na zuwa a dai dai lokacin da shugabannin kasashen Afrika ke zargin kotun ta fi mayar da hankali wajen farautarsu. a Cikin shirin Duniyarmu A Yau, Bashir Ibrahim Idris tare da abokan shirinsa sun tattauna akan wannan batu.20/07/201320:56 -
An samu karuwar cin Hanci a Duniya
Wani rahoton kungiyar Transparency International yace an samu karuwar cin hanci a shekaru biyu da suka gabata, wanda ya karya farin jinin mahukunta ga al’ummar duniya musamman bangaren sharia’a da ‘Yan siyasa da kuma ‘Yan sanda. Cikin jerin sahun kasashe 10 da matsalar cin hanci da rashawa ta yi kamari, 8 daga cikinsu, kasashen Afrika ne, a cewar kakakin kungiyar Transparency. Bashir Ibrahim Idiris ya tattauna da abokokan shirinsa game da rahoton13/07/201320:45 -
Juyin Mulkin Sojoji a Masar
Kasar Masar ta rabu gida biyu bayan da Sojoji suka tumbuke gwamnatin 'Yan uwa Musulmi ta Shugaba Morsi. 'Yan uwa Musulmi sun sha alwashin kalubalantar matakin, a dai dai lokacin da 'Yan adawa a karkashin Mohammed El Baradei ke murnar samun nasara. Wannan shi ne batun da shirin Duniyarmu A yau ya tattauna wanda Bashir Ibrahim Idris ya jagoranta.06/07/201320:17 -
Matsalar Fashin Teku a kasashen Afrika
Hukumar da ke kula da sufurin jiragen ruwa ta duniya tace an samu karuwar fashin jirage a tekun Guinea, wannan matsalar ce kuma ke ci wa kasashen Afrika tuwo a kwarya. Wannan ne dai ya sa Shugabanin Kasashen Afrika ta Yamma, da Afrika ta Tsakiya, suka gudanar da taronsu a Yaoundé a kasar Kamaru, inda suka dauki kudirin kafa rundunar da za ta yi yaki da ‘Yan fashin teku. Shirin Duniyarmu a Yau ya tattauna ne game da wannan batu da kuma illolinsa ga tattalin arzikin kasashen Afrika.29/06/201321:05 -
Matsalar kaucewa biyan haraji a Duniya
Batun inganta tsarin haraji da inganta huldar kasuwanci su ne muhimman batutuwan da Birtaniya ta jagoranta a taron manyan kasashe 8 masu karfin Tattalin arzikin Duniya da suka hada da Amurka da Japan da Jamus da Faransa da Canada da kuma Rasha. Kaucewa biyan haraji matsala ce da ake fuskanta daga attajiran Turai. Shirin Duniyarmu A yau ya tattauna ne akan wannan matsalar ta kaucewa biyan haraji.22/06/201320:36 -
Duniyarmu A yau: Kan zanga-zangar da al'ummar Turkiyya ke yi.
An share tsawon makwanni biyu ana zanga-zanga a kasar Turkiyya, domin nuna rashin amincewa da shirin fasalta wani filin shakatawa da ke birnin Istanbul. Duk da yin amfani da karfi da jami'an tsaro suka yi domin kawo karshen wannan zanga-zanga, hakan ba za ta samu, lamarin da ya sa Firayi Minista Racep Erdogon yin ganawa da wakilan masu zanga-zangar.Bashir Ibrahim Idris da kuma takwarorinsa 'yan jarida, sun tattauna a kan wannan batu na Turkiyya.15/06/201320:36 -
Zargin yin amfani da makami mai guba a rikicin Syria
Kasar Faransa ta ce ta tanadi hujjojin da za su nuna cewa gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba akan 'yan kasarta a fadan da aka tafka a watan Afrilun da ya gabata.09/06/201320:25 -
Rayuwa bayan kafa dokar ta baci a Jihohi uku na Arewacin Najeriya
Duniyarmu A Yau, a wannan mako, Bashir Ibrahim Idirs da kuma wasu 'yan jaridar, sun tattauna ne a game da yadda dokar ta bacin da aka kafa a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa ta shafi rayuwar jama'ar da kuma al'amurran yau da kullum.25/05/201320:20 -
Duniyarmu A yau: Hira da gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko.
A shirin Duniyarmu A Yau na wannan mako, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne da gwamnan jihar Sakkwato da ke Tarayyar Najeriya Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko wanda ya ziyarci Ofishinmu da ke birnin Lagos.18/05/201320:00
Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.