Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Matsalar tsaro a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne akan matsalar tsaro a Najeriya musamman hare haren Boko Haram a yankin arewa maso gabaci da kuma rikicin Fulani.16/03/201420:39 -
Taron kasa a Najeriya: Shiri na biyu
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne dangane da Taron kasa a Najeriya don ba Jama'a damar bayyana korafe korafensu game da yadda ake tafiyar da kasa da kuma zamantakewa. Akwai sabani ra'ayi tsakanin 'Yan Najeriya inda wasu suke ganin taron baya da wani amfani tun da akwai Majalisa lura da tarukan da aka gudanar a shekarun baya. Shirin ya tattauna da 'Yan siyasa masu banbancin ra'ayi akan Taron.08/03/201420:00 -
Taron kasa a Najeriya
Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne dangane da Taron kasa a Najeriya doba ba Jama'a damar bayyana korafe korafensu game da yadda ake tafiyar da kasa da kuma zamantakewa. Akwai sabani ra'ayi tsakanin 'Yan Najeriya inda wasu suke ganin taron baya da wani amfani tun da akwai Majalisa lura da tarukan da aka gudanar a shekarun baya. Shirin ya tattauna da 'Yan siyasa masu banbancin ra'ayi akan Taron.02/03/201420:05 -
Taron Matasan Najeriya domin gina kasa
Shirin Duniyarmu ya tattauna ne da matasa musamman akan taron da wata cibiya ta gudanar a Abuja na matasa akan irin rawar da zasu taka wajen gina kasa.02/02/201420:09 -
Rikicin Syria da Sudan ta Kudu
Shirin Duniyarmu A yau ya tattauna tare da 'Yan Jarida game da rikicin Syria da ke kokarin sasantawa a Geneva tare da diba rikicin Sudan ta kudu inda bangarorin da ke rikici suka amince da matakin tsagaita wuta.26/01/201420:01 -
Dokar haramta auren jinsi guda a Najeriya
Shirin Duniyarmu A yau ya tattauna ne game da dokar haramta auren jinsi guda da shugaban Najeriya ya amince da ita, matakin da kasashen yammaci da majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suke suka.18/01/201420:00 -
Matsalar Tsaro da rikicin kabilanci a Najeriya
Shirin Duniyarmu a yau ya diba matsalolin tsaro ne a Najeriya da rikicin kabilanci da Addini musamman a arewacin Najeriya.11/01/201420:21 -
Dambarwar siyasar Najeriya a 2013
Shirin Duniyarmu a Yau ya diba dambarwar siyasar Najeriya ne a 2013 musamman kafa sabuwar Jam'iyyar adawa ta APC da ke yi wa PDP mai mulki barazana a zaben 2015.04/01/201421:35 -
Dokokin kare hakkin Mata a Katsina
Shirin Duniyarmu a yau ya yi bayani ne akan dokokin kare mata da suka shafi Fyade da 'Yan Majalisar dokoki a Jahar Katsina suka kafa dokokin.21/12/201321:38 -
Martabar Mandela da Wasikar Obasanjo zuwa ga Jonathan
Shirin Duniyarmu A yau ya tattauna ne tare da 'Yan Jaridu akan yadda aka girmama Mandela bayan ya mutu a ranar 5 ga watan Disemba. Shirin kuma ya tabo batun Wasikar da Olusegun Obasanjo ya aikawa Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.15/12/201321:49 -
Gwagwarmayar Nelson Mandela
Shirin Duniyarmu A yau da Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta tare da 'Yan jaridu ya tattauna ne akan gwagwarmayar Tsohon Shugaban Afrika ta kudu wanda ya mutu a ranar Alhamis 5 ga watan Disemba.07/12/201320:29 -
Yajin aikin Malaman Jami'ao'in Najeriya
Shirin Duniyarmu a Yau na wannan mako ya yi dubi ne akan yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ASUU suka kwashe fiye da watanni uku suna yi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin shugabanin kungiyar Farfesa Iyayi yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa wani taro.17/11/201320:50 -
Kalubalen da 'yan jaridu ke fuskanta a duniya
Shirin Duniyarmu a Yau na wannan makon ya tattauna ne akan irin kalubalen da 'yan jaridu ke fuskanta a duniya yayin da suke gudanar da ayyukansu. Kusan makwannin biyu ke nan da aka kashe wasu wakilan tashar RFI faransawa, wato Ghislaine Dupont da kuma Claude Verlon lamarin da ya ja hankulan mutane da dama a duniya.09/11/201320:05 -
Dakarun Congo sun samu nasara akan 'Yan tawaye
Shirin Duniyarmu a yau ya tattauna ne game da nasarar da Dakarun Jamhuriyyar Congo suka samu akan 'Yan tawayen M23 bayan kwashe lokaci ana gwabza yaki.03/11/201320:20 -
Dambarwar Sayen Motoci a Ma'aikatar Sufuri a Najeriya
Shirin Duniyarmu A yau ya tattauna ne da 'Yan Jarida game da dambarbawar sayen Motoci masu sulke da suka wuce kima da Ministan Sufuri Princess Stella Oduah ta saya, lamarin da ya janyo cece kuce a Najeriya da har ya kai kungiyoyin fararen hula suka gudanar da zanga-zanga domin neman a hukunta Ministan. Bashir tare da abokan shirinsa sun tattauna wannan batu.26/10/201321:03
Dandalin Siyasa
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.